Yaki da rashawa: Alkali ya tausaya ma Maina saboda yana zubar da jini a kotu

Yaki da rashawa: Alkali ya tausaya ma Maina saboda yana zubar da jini a kotu

Wata sabuwa ta faru a kotu a ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba a cigaba da sauraron karar tuhume tuhumen cin hanci da rashawa da satar kudaden yan fansho da hukumar EFCC take yi ma tsohon shugaban kwamitin gyaran dokokin fansho, Abdulrashid Maina.

Jaridar The Cables ta ruwaito a zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan wanda ake kara, watau Abdulrashid Maina, Francis Oronsaye ya nemi kotu ta sarara ma Maina saboda bashi da lafiya, har ta kai yana zubar da jini.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai farmaki jahar Filato, sun kashe shugaban Miyetti Allah

Wannan lamari ya fara ne a yayin da kotun ta fara zamanta, yayin da Maina yake zaune tare da iyalansa, da wasu jami’an hukumar gidajen yarin Najeriya dake tsare da shi. Jami’an sun yi kokarin daga Maina a lokacin da kotu ta bukaci a shigar da shi akwatin bada shaida.

Sai dai Alkalin kotun, Okon Abang na babban kotun tarayya dake Abuja ya umarci jami’an a kan su kyale Maina biyo bayan korafi da lauyansa ya mika ma kotu a kan cewa Maina ba shi da lafiya, don haka yake rokon alfarmar kotu ta bashi dama ya sha magungunansa.

“Ya mai sharia, wanda nake karewa ba shi da lafiya, jini na fita daga jikinsa, ina rokon kotu mai adalci ta bashi daman shan magungunansa.” Inji Alkalin.

Da wannan ne Alkalin ya umarci Maina ya yi zamansa a inda yake, sa’annan ya sanar da hutun mintuna 20 kafin kotu ta cigaba da zaman sauraron shari’ar.

Idan za’a tuna, Maina na fuskantar tuhume tuhumen karkatar da kimanin kudi naira biliyan biyu mallakin yan fansho, sa’annan ya tsere domin kauce ma shiga hannun jami’an tsaro, har sai a watan Oktoba jami’an DSS suka samu nasarar kama shi bayan tsawon shekaru 4 yana gudun tsira.

Bayan kama Maina sai babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta bada umarnin kwace wasu manyan kadarorinsa guda 23 da suka hada da gidaje, filaye da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel