Kano: Zanga-zanga ta barke a kan sauke sabbin sarakunan Ganduje

Kano: Zanga-zanga ta barke a kan sauke sabbin sarakunan Ganduje

- Wasu mazauna jhar Kano sun tada zanga-zanga a kan rasshin gamsuwa da hukuncin kotu a yau

- Kotun ta yanke hukuncin tube rawunan sabbin Sarakunan da gwamnatin jihar ta nada ne tare da soke masarautunsu

- A halin yanzu dai gwamnatin jihar Kano na da kwanaki 90 don daukaka kara, rashin yin hakan na nufin ta gamsu da hukuncin

Wasu mazauna jihar Kano sun tada zanga-zanga a kan sauke sabbin sarakunan jihar Kano da kotu ta yi a yau. Masu zanga-zangar sun nuna rashin jin dadinsu a kan wannan cigaban. Sun ce wannan yunkuri ne na dakile karuwar da suke yi daga sabbin masarautun da suke ta mora.

A yau Alhamis ne wata babban kotu da ke zama a jihar Kano ta soke kirkirarrun sarakuna 4 da masarautunsu na jihar Kano.

Alkalin kotun, Jastis Usman Na'Abba, ya yanke hukuncin cewa kirkirar masarautun tare da nada sarakunan masu darajar farko an yi ne ba bisa ka'ida ba.

Hakan na nufin yanzu sarki daya ne a jihar Kano.

DUBA WANNAN: Ganduje-Sanusi: Kotu ta rushe sabbin sarakunan da Ganduje ya kirkira a Kano

Sabbin Sarakunan da aka tube wa rawuna sun hada Aminu Ado Bayero, wanda shine Sarkin Bichi. Ibrahim Abubakar a matsayin Sarkin Karaye, Tafida Abubakar II a matsayin Sarkin Rano da kuma Ibrahim Abdulkadir a matsayin Sarkin Gaya.

A halin yanzu dai gwamnatin jihar Kano na da kwanaki 90 don daukaka kara. Yin shirunta kuwa na nufin ta gamsu da hukuncin kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel