Farfesa Osinbajo ya jagoranci gwamnoni 36 a zaman majalisar tattalin arziki

Farfesa Osinbajo ya jagoranci gwamnoni 36 a zaman majalisar tattalin arziki

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar tattalin arziki ta kasa daya gudana a ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa mataimakin shugaban kasa shi ne shugaban wannan majalisa na tattalin arziki.

KU KARANTA: Yan majalisa sun amince ma Buhari ya kara nau'o'in haraji guda 7 ga yan Najeriya

Wannan majalisa aikinta shi ne kula da tsare tsaren tattalin arzikin kasa a dukkanin matakan gwamnati, haka zalika kudin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi majalisar ta dinga zama sau daya a kowanne wata domin tattaunawa a kan tattalin arzikin kasar.

Majalisar ta kunshi kafatanin gwamnonin Najeriya 36, gwamnan babban bankin Najeriya, ministan kudi, sakataren gwamnatin Najeriya da sauran manyan jami’an gwamnati da hukumomin gwamnati da aikinsu ya shafi tattalin arziki.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an fara zaman ne da misalin karfe 12:30 na rana, taron ya samu halartar yawancin gwamnonin Najeriya, yayin da aka hangi mataimakan gwamnonin wasu jahohi sun wakilcin gwamnoninsu. Ana cigaba da gudanar da wannan zama a yayin tattara wannan rahoto.

A wani labarin kuma, majalisar dattawa ta Najeriya, ta Sanatoci masu jajayen kujeru ta amince tare da buga sanda a kan bukatar da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta aika mata na yin gyarar fuska ga dokokin haraji a Najeriya.

Tashin farko, kudurin da majalisar ta amince da shi na tattare da bukatar amincewar majalisar wajen kara harajin kayan masarufi watau VAT, daga kashi 5 zuwa kashi 7.5, kuma majalisar ta amince da shi kai tsaye.

Haka zalika kudurin ya amince da kara wasu nau’o’in haraji guda 7 da suka hada da; harajin a kan kudaden shiga na kamfani, harajin ribar man fetir, harajin shigo da kaya na kwastam, harajin Stamp, harajin kudin dake shigo ma yan Najeriya da kuma harajin kadarori.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel