Hukumar INEC ta baiwa Yahaya Bello takardar shaidar cin zabe

Hukumar INEC ta baiwa Yahaya Bello takardar shaidar cin zabe

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba, ta gabatar da takardar shaidar cin zabe ga Gwamna Yahaya Bello da mataimakinsa, Edward David Onoja a jihar Kogi.

Taron ya gudana ne a babban dakin taro na Farfesa Mahmoud Yakubu, a hedkwatar hukumar zaben da ke Lokoja, babbar birnin jihar.

Bello da Onoja sun yi takara a zaben gwamna da aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sannan kuma sune suka lashe zaben.

APC ta samu kuri’u 406,222 wajen kayar da Musa Wada na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda ya samu kuri’u 189,704.

Kwanishinan zabe na kasa da ke kula da arewa ta tsakiya, Mohammed Kudu Haruna wanda ya gabatar da takardar cin zabe ya zababben gwamnan da mataimakinsa ya ce, “yau ya yi daidai da sabon zubi bayan zabe sannan ana sa ran zababben gwamna da mataimakinsa za su sauke hakkin da ya hau kansu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta saki jadawalin sabon albashi da kowani ma’aikaci zai kwasa (dalla-dalla)

A jawabinsa, Gwamna Bello ya ce yayinda yau ya kasance karo na biyu da yake karban takardar cin zabe a matsayin gwamna, wannan me zai zamo karo na karahe da zai karbi takardar zama gwamna daga hannun INEC.

A wani lamari makamancin haka, mun ji cewa hukumar shirya da zaben kasa mai zaman kanta INEC, ta baiwa zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon, shahadar nasarar zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 16 ga Nuwamba, 2019.

David Lyon, wanda yayi takara karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya lallasa abokan hamayyarsa 44 da dan takarar PDP, Sanata Duoye Diri.

Hakazalika, hukumar ta baiwa wani zababben dan majalisar dokokin jihar Bayelsa mai wakiltar mazabar Brass 1, Charles Daniel.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel