Yanzun nan: Oshiomhole zai gana da manyan masu ruwa da tsaki na APC a majalisar wakilai

Yanzun nan: Oshiomhole zai gana da manyan masu ruwa da tsaki na APC a majalisar wakilai

- Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole zai gaba da manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a majalisar wakilai

- Ahmed Wase, mataimakin kakakin majalisar wakilai ne ya sanar da hakan a lokacin da ya jagoranci zaman majalisar a yau Alhamis

- Ya ce an shirya gudanar da taron ne da misalin karfe 3:00 na rana

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole zai gaba da manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a majalisar wakilai.

Mataimakin kakakin Majalisar, Ahmed Wase, ne ya sanar da hakan a lokacin da ya jagoranci zaman majalisar a yau Alhamis, 21 ga watan Nuwamba.

Ya bayyana cewa an shirya gudanar da taron ne da misalin karfe 3:00 na rana.

KU KARANTA KUMA: Zabukan Bayelsa da Kogi: An matsawa Secondus kan ya yi murabus

A wani lamarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa gabanin zaman jigogin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da zai gudana yau a fadar shugaban kasa Villa da kuma zaman majalisar zantarwan jam'iyyar da zai gudana gobe Juma'a, wasu mambobin jam'iyyar sun dira hedkwatar APC dake Abuja.

Matasan suna gudanar da zanga-zangar bukatan shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomole, yayi murabus ko a tsigeshi karfi da yaji.

Masu zanga-zangan sun yi ikirarin cewa maimakin Oshiomole ya dabbaka kundin tsarin mulkin jam'iyyar, shine kan gaba wajen saba mata, kuma hakan ya janyo rabuwan kai tsakanin 'yayan jam'iyya musamman a jihar Edo.

Sun yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari, babban jigon jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, da sauran shugabannin jam'iyyar sun tabbatar da cewa Adams Oshiomole ya yi murabus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel