Yan majalisa sun amince ma Buhari ya kara nau'o'in haraji guda 7 ga yan Najeriya

Yan majalisa sun amince ma Buhari ya kara nau'o'in haraji guda 7 ga yan Najeriya

Majalisar dattawa ta Najeriya, ta Sanatoci masu jajayen kujeru ta amince tare da buga sanda a kan bukatar da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta aika mata na yin gyarar fuska ga dokokin haraji a Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito a ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba ne majalisar ta amince da kudurin ‘sha’anin kudi’ wanda ya bata daman yin kwaskwarima tare da garambawul a kan dukkanin dokokin haraji da ake biya a Najeriya.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Buhari ya rattafa hannu kan dokar haramta ba-haya a bainar jama’a

Sai dai a tashin farko, kudurin da majalisar ta amince da shi na tattare da bukatar amincewar majalisar wajen kara harajin kayan masarufi watau VAT, daga kashi 5 zuwa kashi 7.5, kuma majalisar ta amince da shi kai tsaye.

Haka zalika kudurin ya amince da kara wasu nau’o’in haraji guda 7 da suka hada da; harajin a kan kudaden shiga na kamfani, harajin ribar man fetir, harajin shigo da kaya na kwastam, harajin Stamp, harajin kudin dake shigo ma yan Najeriya da kuma harajin kadarori.

Sai dai an samu wasu Sanatoci da suka nuna tirjiya da wannan kudurin, watau Sanata Enyinnaya Abaribe, Ifeanyi Ubah, Gabriel Suswam da Abba Moro da suka nuna rashin amincewa da kuduri, inda suka ce amincewa da kudurin zai jefa yan Najeriya cikin karin wahalhalu.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattafa hannu a kan dokar haramta ba-haya a bainar jama’a, dokar da aka yi ma take da ‘Executive order 009’ a turance, tare da nufin kawo karshen kashi a waje a shekarar 2025.

Shugaban kasa ya rattafa sa hannunsa a kan wannan doka ne a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba a ofishinsa dake fadar gwamnatin Najeriya, inda yace akwai bukatar magance wannan matsala duba da cewa Najeriya ce kasa ta biyu da ta shahara wajen kashi a waje.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel