Da duminsa: Buhari ya shiga ganawa da shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36

Da duminsa: Buhari ya shiga ganawa da shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36

Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36 a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, 21 ga Nuwamba, 2019.

An fara zaman ne misalin karfe 11 na safe.

Yan majalisun sun dira Abuja ne karkashin jagorancin kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa.

A hirar da yayi da manema labarai bayan ganawar, Mudashiru Obasa, ya laburta cewa kundin tsarin mulki ta baiwa majalisun dokokin jiha karfin zaman kansu amma gwamnoni na kin aiwatarwa.

Ya yi kira da shugaba Buhari ya kawo dauki domin ganin cewa an tilastawa gwamnoni aiwatar da hakan.

"Muna kira ga shugaban kasa ya sanya baki domin gaggauta aiwatarwa. Mun bashi shawaran cewa ya bada umurnin kai tsaye domin tabbatar da hakan." Yace

KU KARANTA: Hukumar INEC ta baiwa David Lyon shahadar nasaran zabe

Bugu da kari, yan majalisun sun bukaci rage karfin gwamnatin tarayya ta hanyar mayar da iko hannun jihohi da kananan hukumomi.

Daga cikin wadanda ke cikin ganawar sune kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila; sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; ministan labarai, Lai Mohammed, da CoS, Abba Kyari.

Kalli hotunan:

Da duminsa: Buhari ya shiga ganawa da shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36

Da duminsa: Buhari ya shiga ganawa da shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel