EPL: Tottenham ta ribanyawa Mourinho abin da ta ke biyan Pochettino

EPL: Tottenham ta ribanyawa Mourinho abin da ta ke biyan Pochettino

Jose Mourinho wanda ya ke yi wa kansa da lakabin na musamman, zai rika karbar albashin da ya ninka abin da aka rika biyan Mauricio Pochettino lokacin da ya ke horas da Tottenham.

Rahotanni daga Jaridar Sun sun bayyana cewa Jose Mourinho zai rika samun kudi fam miliyan £15 duk shekara a Tottenham. Hakan na nufin duk wata Mourinho ya na da fam miliyan 1.25.

Idan aka yi lissafin wannan kudi a Naira a yau, za a ga cewa abin da sabon Kocin na Tottenham zai rika karba a duk wata shi ne N586,343,750. Albashinsa na shekara ya haura Naira biliyan 7.

Abin da aka rika biyan Mauricio Pochettino lokacin ya na kulob din a shekara shi ne fam miliyan £7.5. Wannan na nufin duk kasar Ingila, Pep Guardiola ne kadai ya fi Mourinho karfin albashi.

Ana tunanin cewa Kocin na Manchester City, Pep Guardiola, ya kan tashi da fam miliyan £20 a shekara bayan ya taimakawa Manchester City wajen lashe gasar Firimiya na Ingila biyu a jere.

Jose Mourinho ne na biyu a wannan jerin yayin da Magajinsa a Manchester, Ole Gunnar Solskjaer ya ke biye a kan fam miliyan 7.5. Wannan shi ne abin da Liverpool ta ke biyan Jurgen Klopp.

KU KARANTA: Tottenham ta dauki hayar Jose Mourinho na shekaru hudu

Tsohon Kocin Manchester City, Manuel Pellegrini, shi ne na biyar a wannan lissafi. Asusun Koci Pellegrini ya kan motsa da fam miliyan £7 duk karshen shekara a kungiyarsa ta West Ham.

Sabon Kocin Arsenal, Unai Emery wanda ya bar PSG kwanakin baya yak an karbi fam miliyan £6 a Landan. Wannan shi ne abin da Southampton ta ke biyan Ralph Hasenhuttl mai shekara 52.

Tsohon yaron Jose Mourinho, Frank Lampard zai rika karbar fam miliyan £5.5 a Chelsea. A bayan sabon shigan Kocin akwai Brendan Rodgers da Eddie Howe a kan fam miliyan £5 da kuma £54.

Jerin kamar yadda jaridar The Sun ta rahoto:

1. Pep Guardiola

2. Jose Mourinho

3. Ole Gunnar Solskjaer

4. Jurgen Klopp.

5. Manuel Pellegrini

6. Unai Emery

7. Ralph Hasenhuttl

8. Frank Lampard

9. Brendan Rodgers

10. Eddie Howe

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel