Kwangilolin bogi: Ka lalubi Ministocinka – Sanatocin PDP ga Buhari

Kwangilolin bogi: Ka lalubi Ministocinka – Sanatocin PDP ga Buhari

A Ranar Laraba, 20 ga Watan Satumban 2019, Sanatocin da ke karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, sun yi kira ga shugaban kasa da ya karkatar da akalarsa ga Ministocinsa.

Sanatocin adawar sun fadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan ne bayan da ya fito ya na zargin ‘yan majalisar da batar da kudi Naira tiriliyan 1 da sunan ayyukan mazabu a bogi.

‘Yan majalisar tarayyan sun kare kansu inda su ka ce Ministoci da shugabannin hukumomin gwamnati za a damke su yi bayanin bacewar wadannan kudin da aka cewa ba a ga aikinsu ba.

Sanata Eyinnaya Abaribe shi ne ya yi wannan jawabi a madadin Abokan aikinsa, ya ce babu mamaki masu rubutawa shugaban kasar jawabi ne su ka yi kuskure wajen ba shi bayanai.

Abaribe ya na cewa ba ‘yan majalisa ba ne su ke da alhakin aiwatar da ayyukan Mazabu. “Mun dade mu na cewa ba Sanatoci ko ‘Yan majalisa su ke aiwatar da kwangilolin mazabu ba.”

KU KARANTA: Za a zartar da hukunci a kan wasu manyan Sanatocin Jam’iyyar APC

Sanatan na PDP ya kuma kara da cewa: “Ana jibge ayyukan ne a ofishin masu zartarwa. Idan shugaban kasa ya ce bai ga komai ba, sai ya tuntubi Ministoci da hukumomin da ke karkashinsa.”

Mai wakiltar shiyyar jihar Abia a majalisar dattawan ya bayyana cewa masu ikon zartarwa ne su ke yin wadannan ayyuka da ake warewa kowace mazaba ta hannun ‘dan majalisar tarayyanta.

A na sa bangaren, Godiya Akwashiki, wanda ke magana a madadin majalisar dattawan ya ce za su fito su yi cikakken jawabi game da wannan idan har shugaban kasar ya rubuta masu takarda.

Sanata Akwashiki ya gaza maida wani martani, sai dai ya buge da cewa: “Shugaban kasa ya yi magana ne, amma ku wani lokaci akwai ku da ban dariya. Idan akwai wani abu, zai aiko mana”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel