Daga karshe Osagie Ize-Iyamu ya sauya sheka daga PDP

Daga karshe Osagie Ize-Iyamu ya sauya sheka daga PDP

Osagie Ize-Iyamu, wani tsohon sakataren gwamnatin jihar Edo a karkashin mulkin Cif Lucky Igbinedion, wanda aka dakatar, ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A wasikar murabus dinsa a ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba, Ize-Iyamu ya bayyana cewa ya jam’iyyar ne duba ga abubuwan da ke faruwa a PDP, jaridar This Day ta ruwaito.

Sai dai ya bayyana cewa hukuncinsa na sauya sheka daga jam’iyyar bai kasance da gaba ba, domin a cewarsa ba zai iya nuna yatsa ga wata jam’iyya wacce ya ci moriyarta ba a baya.

Ize-Iyamu ya kara da cewa burinsa a koda yaushee shine wakiltan mutanen jihar a siyasa da kuma tabbatar da cewa anyi amfani da manufofin gwamnati wajen inganta rayukan talakawa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa mafarkin Fasto Osagie Ize-Iyamu na son zama gwamnan jihar Edo na iya zama gaskiya yayinda aka rahoto cewa ya kammala shiri tsaf domin barin PDP zuwa APC.

Ize-Iyamu ya kasance tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna na 2016.

Kafin komawarsa PDP, tsohon sakataren gwamnatin na jihar Edo a lokacin tsohon gwamna Lucky Igbinedion ya bar Oshiomhole lokacin da ya fito yace ba zai marawa kudirinsa baya ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta saki jadawalin sabon albashi da kowani ma’aikaci zai kwasa (dalla-dalla)

A wani labarin kuma Legit.ng ta rahoto cewa wasu mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi kira ga Shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus da ya yi murabus daga matsayinsa.

An tattaro cewa sun yi wannan kiran ne kan zargin saba kundin tsarin jam’iyya, almubazaranci da kudade da kuma gaza jagorantar jam’iyyar zuwa ga tafarkin nasara a zabukan 2015 da 2019. Kari kan haka, mambobin na PDP sun kuma yi zargin cewa Secondus ya gaza kiran babban taro na jam’iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel