Da duminsa: Hukumar INEC ta baiwa David Lyon shahadar nasaran zabe

Da duminsa: Hukumar INEC ta baiwa David Lyon shahadar nasaran zabe

Hukumar shirya da zaben kasa mai zaman kanta INEC, ta baiwa zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon, shahadar nasarar zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 16 ga Nuwamba, 2019.

David Lyon, wanda yayi takara karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya lallasa abokan hamayyarsa 44 da dan takarar PDP, Sanata Duoye Diri.

Hakazalika, hukumar ta baiwa wani zababben dan majalisar dokokin jihar Bayelsa mai wakiltar mazabar Brass 1, Charles Daniel.

Kwamishanan INEC na jihar Bayelsa, Monday Udoh, ya bayyana cewa duniya ta shaida cewa lallai an gudanar da zaben kwarai a jihar Bayelsa.

DUBA NAN Matasa sun cika hedkwatan APC a Abuja suna yiwa Oshiomole iwun 'Bamaso'

Mun kawo muku rahoton cewa David Lyon ya lashe kuri'un kananan hukumomi shida yayinda babban abokin hamayyarsa na PDP, Duoye Diri, ya kashe kananan hukumomi biyu.

Nasarar Lyon ta karya tarihin mulkin PDP a jihar na tsawon shekaru 20 tun 1999 da aka dawo da emokradiyya Najeriya.

Baturen zaben jihar Bayelsa, Farfesa Faraday Orumwense, ya bayyana sakamakon cewa Lyon ya samu jimillar kuri'u 352,552 yayinda Diri ya samu kuri'u 143,172.

Kananan hukumomin da APC ta lallasa PDP sun hada da Brass; Nembe; Ogbia, Southern Ijaw, Ekeremor da Yenagoa yayinda PDP ta samu Sagbama da Kolokuma/Opokuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel