Yanzu-yanzu: Matasa sun cika hedkwatan APC a Abuja suna yiwa Oshiomole iwun 'Bamaso'

Yanzu-yanzu: Matasa sun cika hedkwatan APC a Abuja suna yiwa Oshiomole iwun 'Bamaso'

Gabanin zaman jigogin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da zai gudana yau a fadar shugaban kasa Villa da kuma zaman majalisar zantarwan jam'iyyar da zai gudana gobe Juma'a, wasu mambobin jam'iyyar sun dira hedkwatar APC dake Abuja.

Matasan suna gudanar da zanga-zangar bukatan shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomole, yayi murabus ko a tsigeshi karfi da yaji.

Masu zanga-zangan sun yi ikirarin cewa maimakin Oshiomole ya dabbaka kundin tsarin mulkin jam'iyyar, shine kan gaba wajen saba mata, kuma hakan ya janyo rabuwan kai tsakanin 'yayan jam'iyya musamman a jihar Edo.

Sun yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari, babban jigon jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, da sauran shugabannin jam'iyyar sun tabbatar da cewa Adams Oshiomole ya yi murabus.

DUBA NAN: Hukumar INEC ta baiwa David Lyon shahadar nasaran zabe

A watan Oktoba, An samu tashin hankali a jihar Edo ranar Lahadi sakamakon rahoton cewa an kai hari gidan shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, Adams Oshiomhole.

Wasu fusatattun matasa sun dira gidan Adams Oshiomole inda suke ihun 'Oshiomole barawa Oshiomole barawo' amma yan sanda sun fitittikesu.

Mai magana da yawun Oshiomole, Mista Simon Ebegbulem, ya bayyana cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ne ya tura yan daba su ci mutucinsa.

Ya ce wannan hari da suka kai na daya daga cikin shawarin da aka yanke a taron majalisar zantarwan jihar na cin mutuncin duk wadanda basu goyon bayan tazarcen gwamnan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel