Gwamnatin tarayya ta saki jadawalin sabon albashi da kowani ma’aikaci zai kwasa (dalla-dalla)

Gwamnatin tarayya ta saki jadawalin sabon albashi da kowani ma’aikaci zai kwasa (dalla-dalla)

Kungiyar kwadago ta TUC ta tabbatar da jadawalin gwamnatin tarayya kan sabon karancin albashin ma’aikata.

Jadawalin daga gwamnati na dauke da sa hannun Ekpo Nta, mukaddashin Shugaban hukumar kudin shiga na kasa, albashin ma’aika, sannan an tura kwafinsa zuwa ga Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kai da kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, jaridar The Nation ta ruwaito.

Da yake magana kan cigaaban, Shugaban kungiyar TUC, Quadri Olaleye, ya bayyana cewa sun karbi takardar sannan sun aika zuwa ga kungiyoyinsu na jiha domin nusar dasu yarjejeniyar.

Kamar yadda ya ke a jawalin, abunda kowani ma’aikacin gwamnati zai dunga dauka duk shekara zai kama kamar haka:

Level 1 step 1 zai kwashi N360,000 duk shekara

Level 1, step 15 zai kwashi N422, 566 duk shekara

Level 5, step 1 zai kwashi N394, 498 duk shekara sannan step 15 zai kwashi N534, 834 duk shekara

Level 7, step 1 zai kwashi N638, 133 duk shekaa sannan step 5 zai kwashi N961, 577 duk shekara

Level 10 step 1 zai kwashi N1, 060,833 duk shekara yayinda step 15 na wannan matakin zai kwashi N1, 535,417 duk shekara

KU KAANTA KUMA: Zabukan Bayelsa da Kogi: An matsawa Secondus kan ya yi murabus

Level 14, step 1 zai kwashi N1, 503,149 duk shekara yayinda step 11 na wannan matakin zai kwashi N2, 101,600 duk shekara

Level 17 step 9 zai tashi da N6,215,435 duk shekara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel