Yanzu-yanzu: Maina ya iso kotu domin cigaba da shari'arsa

Yanzu-yanzu: Maina ya iso kotu domin cigaba da shari'arsa

Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul (PRTM) a yau Alhamis ya iso babban kotun tarayya da ke Abuja a zaman da za ayi na cigaba da sauraron shari'ar tuhumar da ake masa.

Duk da cewa a yau Maina ba zo kotun a kan kujerar marasa lafiya ba, wasu mutane biyu ne suka taimaka masa ya shigo kotun sune rike da shi kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Tsohon shugaban ta PTRM ya iso kotun n misalin karfe 9.30 na safe sanye da kaftani fari da bakar hula.

Dansa, Faisal, shima yana kotun domin cigaba da sauraron shari'arsa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa Mai shari'a Okon Abang a ranar 7 ga watan Nuwamba ya tsayar da yau 21 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a cigaba da sauraron shari'ar bayan rokon da mataimakin kwantrolla na bangaren lafiya da walwalar hukumar gidajen gyaran hali na kasa, H.B. Kori ya nemi kotun ta bashi mako guda domin ya amsa tambayar da kotun ta masa kan lafiyar Mista Maina.

DUBA WANNAN: Rufe iyakoki: Duk wanda ba zai ci shinkafar 'gida' ba matsalarsa ne - Sanata Adamu

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ne ta gurfanar da Mista Maina tare da wani kamfani mai suna Common Inout Property and Investment Ltd a gaban Mai shari'a Abang a ranar 25 ga watan Oktoba.

Ana tuhumarsa da laifuka 12 masu alaka da almundahar kudi, damfara da mallakar asusun ajiyar banki na bogi.

NAN ta ruwaito cewa Maina ne wanda aka yi kara na farko yayin da kamfanin kuma ita ce wanda aka yi kara ta biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel