Da dumi dumi: Buhari ya rattafa hannu kan dokar haramta ba-haya a bainar jama’a

Da dumi dumi: Buhari ya rattafa hannu kan dokar haramta ba-haya a bainar jama’a

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattafa hannu a kan dokar haramta ba-haya a bainar jama’a, dokar da aka yi ma take da ‘Executive order 009’ a turance, tare da nufin kawo karshen kashi a waje a shekarar 2025.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban kasa ya rattafa sa hannunsa a kan wannan doka ne a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba a ofishinsa dake fadar gwamnatin Najeriya, inda yace akwai bukatar magance wannan matsala duba da cewa Najeriya ce kasa ta biyu da ta shahara wajen kashi a waje.

KU KARANTA: Kulawa da walwalar ma’aikata shine babban abin dake gabana a yanzu – Buhari

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kasa yana kokawa da cewa alkalumma sun bayyana yan Najeriya mutum miliyan 46 ne suka kashi a waje ba tare da shiga cikin bandaki ba, don haka ake samun koma baya a kasar wajen cimma muradun karni a Najeriya.

Shugaban kasa Buhari ya bayyana wasu matakai da gwamnati za ta dauka domin kawo karshen ba-haya a bainar jama’a, inda yace gwamnati za ta dabbaka tsarin samar da isashshen ruwa a Najeriya da kuma samar da makewayi.

“Dokar ta fara aiki ne daga ranar Laraba, muna fatan kawo karshen ba-haya a bainar jama’a daga yanzu zuwa shekarar 2025 a Najeriya gaba daya, tare da hadin gwiwar ma’aikatar ruwa da sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya.

“Dokar za ta tabbatar da an samar da makewayi a dakunan ba-haya a makarantu, otal otal, gidajen mai, wuraren bauta, kasuwanni, asibitoci da ofisoshi.” Inji shi.

A wani labari kuma, shugaba Buhari ya karrama wani babban jami’in hukumar kwastam, Bashir Abubakar, mai mukamin mataimakin kwanturolan kwastam sakamakon kin karbar cin hancin makudan kudi da masu fasa kauri suka bashi.

Shi dai Abubakar ya ki amincewa da cin hancin $412,000, kimanin N149,350,000 da wasu mutane suka bashi kimanin watanni 8 da suka gabata domin su shigo da sundukai guda 40 na kwayar nan mai sa maye watau Tramadol.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel