Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai wa Kwamishina hari, sun kashe direbansa

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai wa Kwamishina hari, sun kashe direbansa

Wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a gano ko su wanene ba sun kai wa Kwamishinan Filaye na jihar Oyo, Abdulraheem Abiodun hari inda suke kashe direbansa.

Mai tsaronsa shima ya samu rauni yayin harin kuma a halin yanzu yana asibiti yana samun kulawa sakamakon harbinsa da su kayi da bindiga.

Channels Television ta ruwaito cewa harin ya faru ne a daren jiya Laraba misalin karfe 8 na dare bayan an ajiye kwamishinan a gidansa dake Ibadan, babban birnin jihar.

DUBA WANNAN: Rufe iyakoki: Duk wanda ba zai ci shinkafar 'gida' ba matsalarsa ne - Sanata Adamu

Kawo yanzu dai ba a san anihin dalilin da yasa 'yan bindigan suka kaiwa kwamishinan harin ba.

Rundunar 'yan sanda a jihar ta ce za ta kira taron manema labarai anjima domin yin karin bayani kan afkuwar lamarin.

Ku saurari cikakken bayanin ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel