Zabukan Bayelsa da Kogi: An matsawa Secondus kan ya yi murabus

Zabukan Bayelsa da Kogi: An matsawa Secondus kan ya yi murabus

- An matsawa Prince Uche Secondus kan ya yi murabus daga matsayinsa na Shugaban PDP na kasa

- Wasu manyan PDP na so hukumomin EFCC, ICPC da SSS su bincike shi

- A cewarsu, Secondus ba zai iya kai jam’iyyar ga nasara bat a kowani bangare

Wasu mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi kira ga Shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus da ya yi murabus daga matsayinsa.

An tattaro cewa sun yi wannan kiran ne kan zargin saba kundin tsarin jam’iyya, almubazaranci da kudade da kuma gaza jagorantar jam’iyyar zuwa ga tafarkin nasara a zabukan 2015 da 2019.

Karin kan haka, mambobin na PDP sun kuma yi zargin cewa Secondus ya gaza kian babban taro na jam’iyyar.

A cewar Malam Nasir Zahradeen, wani tsohon mai bayar da shawara na musamman kan harkokin jama’a ga tshon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan, mafi akasarin yan PDP na son Secondus ya yi muabus.

KU KARANTA KUMA: Babu Gwamna ko guda da ke goyon bayan kisa a matsayin hukuncin kalamun kiyayya

Ya ci gaba da bayyana cewa suna so hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da ICPC da SSS su bincike shi.

Ya yi zagin cewa Secondus ya taba kudaden jam’iyya, lamarin da ya kasance ba karbabbe ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel