Yansanda sun ceto shanu 273, sun kama barayin shanu guda 7 a Kaduna

Yansanda sun ceto shanu 273, sun kama barayin shanu guda 7 a Kaduna

Rundunar Yansandan jahar Kaduna ta sanar da kama wasu mutane 7 da take zarginsu da satar shanu, tare da kwato dabbobi guda 273 a kauyen Ice dake kusa da garin Kasuwan Magani cikin karamar hukumar Kajuru.

Mataimakin kwamishinan Yansandan Kaduna, Onah Sunday ne ya bayyana haka a ranar Laraba yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Kaduna, inda yace Yansanda sun samu wannan nasara ne a ranar 19 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Babban magana: Dino Melaye ya mika ma INEC bidiyo 21 dake nuna yadda APC ta yi magudi

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Sunday yace sun samu wannan nasara ne sakamakon taimakon aikin tsaro irin na yan doka da jama’a suke dabbakawa a yankin.

“Mun bayyana a yau ne domin mu nuna muku wasu daga cikin nasarorin da rundunar Yansandan jahar Kaduna ta samu a ranar Talata inda muka kwato shanu 246 da tumaki 27 daga hannun wasu barayi da suka sace su, a yanzu haka mun kama barayin su bakwai.

“Mun samu sahihin rahoto cewa barayin suna kokarin dauke dabbobi zuwa wani wuri na daban, samun rahoto keda wuya muka sha gabansu a daidai kauyen Ice dake kusa da kasuwan Magani cikin karamar hukumar Kajuru.

“Sa’annan mun kama barayin dabbobin su 7, wanda a yanzu haka suna bamu hadin kai a binciken da muke gudanarwa. Ina kira ga jama’a dasu dage wajen taimaka ma Yansanda da bayanai masu inganci domin tabbatar da tsaro a yankunansu.” Inji shi.

Daga karshe DCP Sunday Onah ya karkare jawabinsa da bayyana cewa zasu gurfanar da barayin gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike a kansu, sa’annan zasu mika dabbobin ga masu su, amma fa sai sun gabatar da kwakkwaran shaida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel