Babu Gwamna ko guda da ke goyon bayan kisa a matsayin hukuncin kalamun kiyayya

Babu Gwamna ko guda da ke goyon bayan kisa a matsayin hukuncin kalamun kiyayya

Gwamnonin jihohi 36 na kasar karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya, sun bayyana cewa babu Gwamnan da ya fito ya marawa kudirin yanke hukuncin kisa kan masu kalaman kiyayya baya.

Sun kuma bayyana cewa gwamnatocin jiha Za su yanke hukunci kan lamarin karancin albashin ma’aikata zuwa Disamba domin ana kan aiki a kai.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba a karshen taron gwamnonin, mataimakin Shugaban kungiyar kuma Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bayyana cewa babu Gwamnan da ya fito sarari ya goyi bayan yanke hukuncin kisa ga kalaman kiyayya.

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai bayan taron, Tambuwal wanda ya bukaci majalisar dokokin tarayya da ta gudanar da zauren jin ra’ayoyin jama’a kan kalaman kiyayya ya bayyana cewa ya zama dole a dauki ra’ayoyin al’umma da muhimmanci.

Taron ya samu halartan gwamnonin Bauchi, Sokoto, Yobe, Zamfara, Kebbi, Nasarawa, Niger, Imo, Adamawa, da Kwara.

Sauran jihohin da suka samu wakilcin mataimakan gwanoni sun hada da Gombe, Enugu, Edo, Rivers, Akwa Ibom, Oyo, Ebonyi, da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Sagay: Buhari ya nemi Sanatoci su sake tantance Magu domin aikinsa na kyau

A wani labai na daban, mun ji cewa Majalisar NWC ta yi na’am da shirin gina sabuwar sakatariyar jam’iyyar APC.

Bayan nan kuma APC za ta kafa wata cibiya kamar yadda aka tsara. Wannan ya na cikin batutuwan da za a tattauna a zaman NWC da za ayi yau Ranar Alhamis, 21 ga Watan Nuwamban 2019. Za ayi wannan zama ne an jima kadan a babban birnin tarayya Abuja.

Bayan nan, NWC ta nada wani kwamiti na mutum 5 da za su shawo kan rikicin ake yi a jihar Edo. Gwamna Abdullahi Ganduje ne zai jagoranci kwamitin tare da Takwaransa, Aminu Masari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel