Maharaj Ji: Tinubu da Peter Obi sun cancanta da su su zama Shugaban kasa

Maharaj Ji: Tinubu da Peter Obi sun cancanta da su su zama Shugaban kasa

Shugaban kungiyar nan ta One Love Family, Satguru Maharaj Ji, ya bayyana Bola Tinubu da cewa ya cancanci ya zama shugaban kasa idan ana neman ‘dan siyasa daga Kudancin Najeriya.

Satguru Maharaj ya bayyana wannan ne a wajen wata ganawa da yayi da ‘yan jarida a Kauyensa na Maharji Ji kamar yadda NAN ta rahoto. Maharaji ya ziyarci Kauyen ne domin wani taron biki.

A cewarsa: “Kowa ya na iya zama shugaban kasa muddin ya sa kishin kasa a gaban kishin kashin kansa. Idan akwai wanda ya dace da mulki daga Kudancin Najeriya, shi ne Bola Ahmed Tinubu.”

“Zan mika masa mulki idan Kudu maso Yamma za ta fito da shugaban kasa. Abin da ya sa kuwa shi ne ya yi aiki a matsayin mai gayyar jama’a da kuma hada-kan jama’a a fadin kasar nan.”

Malamin ya kuma kara da cewa: “Haka zalika Peter Obi ma zai yi kyau da mulki daga Kudu maso Gabas.” Peter Obi shi ne wanda ya tsaya a takarar mataimakin shugaban kasa a PDP a zaben 2019.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa Jonathan ya bari APC ta karbe Bayelsa - Sule

Maharaj Ji ya kuma shaidawa hukumar dillacin labarai cewa a hikakanin gaskiya babu wata matsala tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Wannan Malami ya ce rade-radin wasu mutane ne kurum ya ke yawo a gari domin jawo sabani tsakanin shugabannin. A baya, ana ta jita-jitar cewa gwamnatin Buhari ta ragewa Osinbajo iko.

NAN ta ce wannan Bawan Allah ya bada shawarar yadda za a shawo kan matsalar ilmi ta hanyar ba jama'a bashin kudi su yi karatu, kuma su biya bayan sun kammala makaranta, sun fara aiki.

A karshe ya nuna goyon bayansa kan rufe kan iyokoki da aka yi, amma ya nemi a duba koken jama’a. Majaraji Ji ya roki Makiyaya sun janye barazanar da su ke yi wa gwamnonin Kudu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel