Sagay: Buhari ya nemi Sanatoci su sake tantance Magu domin aikinsa na kyau

Sagay: Buhari ya nemi Sanatoci su sake tantance Magu domin aikinsa na kyau

Shugaban kwamitin da ke ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan yaki da satar dukiyar kasa, Itse Sagay, ya yi kira ga Mai gidan sa a sake tura sunan Ibrahim Magu a majalisa.

Farfesa Itse Sagay ya nemi shugaban kasar ya bukaci a tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin takaimaimen shugaban EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa.

Itse Sagay ya bayyana wannan ne a lokacin da ya ziyarci Mukaddashin shugaban hukumar na EFCC a ofishinsa da ke Abuja. Sagay ya jagoranci sauran ‘yan kwamitin na sa ne zuwa EFCC.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto mana dazu, Itse Sagay ya bayyana cewa Ibrahim Magu ya nuna tsayawa tsayin-daka da jajircewa tun da ya hau kan babbar kujerar EFCC a shekarar 2015.

KU KARANTA: Abin da ya hana mu tabbatar da Magu a kujerar EFCC - Saraki

“EFCC (a karkashin Magu) ta zama hukumar da ta fi kowace a da da kuma yanzu kokari wajen yaki da rashin gaskiya. Idan abu mai kyau ne, ina tunanin babu adalci ace kuma a nemi wani.”

”A ganimu, mukaddashin shugaba (na EFCC) ya cancanci komai, har a tabbatar da shi a matsayin takamaimen shugaba. Magu mutum ne wanda bai daga kafa kan maganar rashin gaskiya.”

Itse Sagay a madadin kwamitin na sa mai ba shugaban kasa Buhari shawara, ya kara da cewa: “Idan ana maganar rashin gaskiya, mu (PACAC) na tare da shi da hukumar EFCC 100-bisa-100.”

Farfesan ya kuma nuna cewa satar dukiyar kasa ta yi wahala yanzu a Najeriya saboda irin kokarin da ake yi wajen yaki da rashin gaskiya na cin hanci da rashawa a wannan gwamnati.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel