Jam’iyyar APC za ta dauki mataki a kan tsofaffin Gwamnoninta da wasu batutuwa

Jam’iyyar APC za ta dauki mataki a kan tsofaffin Gwamnoninta da wasu batutuwa

Wata jaridar Najeriya ta rahoto cewa Majalisar NWC ta yi na’am da shirin gina sabuwar sakatariyar jam’iyyar APC. Bayan nan kuma APC za ta kafa wata cibiya kamar yadda aka tsara.

Wannan ya na cikin batutuwan da za a tattauna a zaman NWC da za ayi yau Ranar Alhamis, 21 ga Watan Nuwamban 2019. Za ayi wannan zama ne an jima kadan a babban birnin tarayya Abuja.

Bayan nan, NWC ta nada wani kwamiti na mutum 5 da za su shawo kan rikicin ake yi a jihar Edo. Gwamna Abdullahi Ganduje ne zai jagoranci kwamitin tare da Takwaransa, Aminu Masari.

Sauran ‘yan wannan kwamiti sun hada da tsofaffin gwamnonin jam’iyyar; Abiola Ajimobi; Kashim Shettima. Sai kuma Ahmed Wadada a matsayin Magatakardan wannan kwamitin sulhu.

Batun hukunta wasu manyan jam’iyyar ya na cikin abubuwan da za a tattauna a zaman. An dade da dakatar da jiga-jigan jam’iyyar na yankin Arewa, Inuwa Abdulkadir da Lawal Shu’aibu.

KU KARANTA: Na sadaukar da nasasar da na samu ga tsohuwa ta - Bello

Bugu da kari, NWC ta dakatar da wasu tsofaffin gwamnonin jam’iyyar; Rochas Okorocha da Ibikunle Amosun. Ana bukatar sa hannun majalisar NEC kafin a tabbatar da wannan dakatarwa.

Za kuma a duba yadda za a cike guraben da aka bari a jam’iyyar bayan da wasu shugabannin jam’iyyar su ka samu mukamai. Daga ciki akwai Mala Buni, Niyi Adebayo da George Moghalu.

Yanzu haka Uwar jam’iyyar APC ba ta Sakataren jam’iyya na kasa, da Mai binciken kudi da kuma shugaban jam’iyya a Kuduncin kasar bayan sun zama gwamna, shugaban NIWA da Minista.

Jaridar ta ce yunkurin samun Kakakin APC, Lanre Issa-Onilu, bai yiwu ba, bayan da ya ki bada amsa game da tambayoyin da aka yi masa a game da wannan zama da za ayi a karshen mako.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel