El-Rufai ya nada Amina Atoyebi, Maiyaki, dsr a cikin Hadimansa

El-Rufai ya nada Amina Atoyebi, Maiyaki, dsr a cikin Hadimansa

Saude Amina Atoyebi ta shiga cikin Hadiman jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. Mai girma Gwamnan ya tabbatar da wannan nadin mukami da ya bada da kansa a dandalin sadarwa na zamani.

Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa Amina Atoyebi ta samu shiga cikin jerin Masu ba sa shawara. Wannan Baiwar Allah za ta taimakawa gwamnan ne da harkokin cigaban al’umma.

Gwamna El-Rufai ya tabbatar da wannan nadi ne a Ranar Laraba 20 ga Watan Nuwamba, 2019, ta shafukansa na sada zumunta. El-Rufai ya ce tun 2012 Amina Atoyebi, ta ke aiki a karkashinsa.

A baya, Amina Atoyebi, ta zama mai yi wa Nasir El-Rufai bincike, kafin ya nada ta a matsayin Sakatarensa kuma babbar Mai taimakawa wajen harkar gudanar da gwamnati a shekarar 2015.

Jawabin gwamnan ya ce tayi aiki a ofishinsa, har wani lokaci ta kan yi aikin PPS watau babban sakataren gwamna. Yanzu za ta yi aiki domin inganta tsare-tsaren gwamnatin tarayya na NSIP.

Wannan sabon mukami zai sa ta rika lura da N-Power, da harkar ciyar da ‘Yan makaranta, da shiryen-shiryen CCT da GEEP domin rage radadin talauci a fadin jihar Kaduna inji gwamnan.

KU KARANTA: Gwamnan Kaduna ya dauki matakin gyara gidajen mari

Atoyebi ta yi karatun Digiri ne a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya inda ta karanci ilmin tattalin arziki. Daga baya ta tafi Coventry a kasar Ingila inda ta yi Digirgir a harkar kasuwanci da talla.

Kakakin gwamnan Kaduna, ya kuma tabbatar da nadin Ahmed Maiyaki wanda shi ne ya kasance mai magana da tsohon gwamna Mukhtar Ramalan-Yero, a matsayin Hadimin Nasir El-Rufai.

Muyiwa Adekeye ya ce Maiyaki zai taimaka wajen harkar hulda da jama’a. Sauran wadanda aka nada a cikin masu ba gwamnan shawara sun hada da Mubarak Abdulkadir, da kuma Umar Yero.

Ragiwar kuma su ne Rebecca Padonu, Samuel Hadwyah, da Umar Abubakar. Sababbin hadiman za su taimaka wajen harkar tattalin arziki, da fasahar ICT da aikin majalisa da dai sauransu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel