San barka: Ahmed Musa ya dauki nauyin karatun matasa 100 A Jami'ar SkyLine dake Kano

San barka: Ahmed Musa ya dauki nauyin karatun matasa 100 A Jami'ar SkyLine dake Kano

- Kyaftin din ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya Ahmed Musa ya dauki nauyin karatun dalibai guda 100 zuwa jami’ar Skyline dake jihar Kano

- Ahmed Musa ya bayyana hakan ne jim kadan bayan jami'ar ta bashi damar zama ambasadan ta

- Dan wasan kwallon ya bayyana yadda ya dauki ilimi da muhimmanci don haka zai taimakawa matasan da basu da karfin zuwa jami'a domin habakashi

Kyaftin din ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya, Ahmed Musa, ya nuna halin jin kai akan matasa marasa karfi bayan da aka bayyanashi a matsayin sabuwar fuskar jami’ar Skyline da ke Kano a jiya Laraba.

Tauraron da ya koma fili a cikin watannan bayan da ya yi jinyar raunin da ya samu, ya yi alkawarin daukar nauyin dalibai guda 100 a sabuwar jami’ar.

“Na yadda da amfanin ilimi. Don haka ina matukar farin cikin shiga wannan kungiya don habaka harkar ilimi. Ina farin cikin sanar da ku cewa, zan dau nauyin dalibai 100 a wannan jami’ar. Bayani zai zo muku ba da dadewa ba,” ya wallafa a shafinshi na Instagram.

KU KARANTA: Musulunci ya samu karuwa: Ambasadan Birtaniya dake kasar Saudiyya ya Musulunta tare da matarshi

Ahmed Musa shi ne dan wasan kwallon kafa na Najeriya da yafi kowanne dan wasa saka kwallo a raga, zai kasance fuskar jami’ar sannan kuma zai taimakawa jami’ar wajen habaka harkokin wasanni.

Ba yau dan wasan ya fara bayyana irin halin jin kai da tausayi ga al’umma ba. A watan Ramadana, dan wasan kwallon kafan ya rarrabawa marasa karfi abinci don su samu yin azumi cikin walwala kamar kowa. Hakan kuwa ya jawo mishi addu’o’I da fatan alheri daga jama’a daban-daban

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel