Mijina da kwaroron roba yake kwanciya dani shine yasa nake neman wadanda za su gamsar dani a titi - Inji wata matar aure

Mijina da kwaroron roba yake kwanciya dani shine yasa nake neman wadanda za su gamsar dani a titi - Inji wata matar aure

- Kotu ta tsinke igiyar auren shekaru 22 a kan cin amana da ha’inci

- Mijin ya koka kan yadda matar ke tafiya ta yi satittika tare da wasu mazan a waje

- Matar ta ce bata gamsuwa da mijinta ne shiyasa take neman maza a waje

Wata mata ta sanar da kotu yadda ta ke ha’intar mijinta ta hanyar yaudarar wasu maza su kwanta da ita don kwantar mata da sha’awa.

Wata kotu a Ibadan, a ranar Litinin ta kashe auren shekaru 22 bayan alhinin yawaitar rashin da’a a zaman auren.

Alkalin Ademola Odunade, yayin yanke hukuncin a kan karar da direba Abiodun Ganiyu ya kawo ta matarshi Mojisola, wacce yake zargi da cin amanarshi – yayi kira ga ma’aurata da su ji tsoron ubangiji tare da mutunta kowacce mu’amala.

Mai kara, Ganiyu yace rayuwa ta yi mishi kunci tun shekaru 13 da suka gabata, bayan da matarshi ta fada mummunar rayuwa.

“Da farko Mojisola ta sanar dani cewa ta tuba kuma an bata mukamin masinja a coci. Wata rana, ta ce ta fara wata ibada ta kwanaki goma kuma ba zata dinga dawowa gida ba. Amma kuma sai ta fara dawowa gida a bige. Na kaiwa iyayenta kara amma bata ji fadansu ba."

“Lokacin da naga shirmenta ya fara yawa, sai na bata shawarar ta dinga shan giyarta a gida. Abinda ya bata mata rai kenan ta fara satittika bata gida. Duk da munyi tsarin iyali, amma ta yi amfani da hakan don kwanciya da maza kala-kala, saboda haka ya mai shari’a, na gaji, a raba mu kawai.”

KU KARANTA: Wata sabuwa: Annabi ya halatta jin kade-kade da wake-wake - Inji Limamin Harami

A bangaren Mojisola kuwa, bata musanta zargin ba kuma ta amsa laifinta. Amma ta ce babu inda zata je da yara shida wadanda suka haifa.

“Ina shan giya ne gudun kada in kashe kaina, kuma ina barin gida in yi wata daya ko fiye da haka. Ina kuma yaudarar maza ne don in kwantar da sha’awata. Abiodun baya gamsar da ni saboda da kwararon roba yake amfani in zamu kwanta.”

A take alkalin ya raba auren tare da ba wa Ganiyu rikon duk yaran shida. Ya bukaci Ganiyu ya ba Mojisola N5,000 don ta kwashe kayanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel