Rainin wayo: Bayan an kama shi da laifin lalata da 'yar gidan matarshi mai shekara biyu, ya ce wai ya zaci matarshi ce

Rainin wayo: Bayan an kama shi da laifin lalata da 'yar gidan matarshi mai shekara biyu, ya ce wai ya zaci matarshi ce

- Hukumar 'yan sandan jihar Akwa Ibom, ta kama wani mutum mai suna Inionbong Moses

- Ana zarginshi ne da lalata da 'yar gidan matarshi da ta zo da ita daga wani gida

- Wanda ake zargin ya ce ba da gangan ya yi ba, ya ganta ne tamkar matarshi sakamakon giyar da ya cika cikinshi da ita

Hukumar 'yan sandan jihar Akwa Ibom, ta cafke wani mutum mai suna Inionbong Moses a kan laifin lalata 'yar gidan matarshi mai shekaru biyu kacal a duniya.

A yayin amsa laifinshi, ya ce ya afkawa yarinyar ne bayan da ya dawo gida a bige kuma yayi zaton matarshi ce.

A kalamanshi: "Ban san abinda ya hau kaina ba. Na dawo gida daga aikin sintiri kuma na dirki ogogoro. Ban san me ya hau kaina ba. Na haye wa 'yar matata da tazo da ita daga wani gidan da tunanin ita ce matar tawa."

"A lokacin da nake kan yarinyar ne mata ta ta shigo ta kama ni dumu-dumu. A take ta kaini kara wajen hukuma. Na roketa amma ta ki hakura. Duk da kuwa ta haifa min da a watanni uku da suka gabata."

KU KARANTA: Tirkashi: Babu Coach din da ya isa ya hanani bautar ubangijina a duniyar nan - Ahmed Musa

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, SP Odiko MacDon, a yayin tsokaci a kan lamarin yace, an kama wanda ake zargin ne yayin da yake lalata da karamar yarinyar.

A halin yanzu yarinyar tana asibiti tana karbar magani, kuma tana samun sauki. A lokacin da aka kama shi a kanta, an hanzarta kaita asibiti ne saboda ciwukan da ta ji sakamakon kokarin shigarta ta karfi da yayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel