A karo na farko: Sanatoci sun yi tsokaci a kan sakamakon zaben Kogi, Bayelsa

A karo na farko: Sanatoci sun yi tsokaci a kan sakamakon zaben Kogi, Bayelsa

- Mambobin majalisar dattijai 'yan jam'iyyar PDP sun yi watsi da sakamakon zaben gwamna a jihar Kogi da Bayelsa

- Shugaba marasa rinjaye a majalisar dattijai, Enyinnaya Abaribe, ya ce sun yi watsi da sakamakon zaben da INEC ta sanar saboda ya saba da zabin jama'a

- Amma, kakakin majalisar dattijai, Godiya Akwashiki, ya ce akwai dokokin zabe na kasa da suka sanar da mutum abin da zai yi idan bai gamsu da sakamakon zabe ba

Mambobin majalisar dattijai ''yan jam'iyyar PDP sun yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar Kogi da Bayelsa, kwanaki bayan INEC ta sanar da shi.

Mambobin jam'iyyar PDP sun bayyana matsayinsu ne ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, yayin wani taro da manema labarai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Da yake magana amadadin sauran sanatocin jami'iyyar, shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai, Sanata Eyinnaya Abaribe, ya ce sakamakon zaben da INEC ta sanar ya matukar dame su.

Abaribe ya bayyana cewa sun yi watsi da sakamakon zaben ne saboda ba shine zabin jama'a ba, ba abinda jama'a zaba INEC ta sanar ba.

"Mun damu matuka da sakamakon zaben jihar Bayelsa da Kogi da INEC ta sanar bayan jama'a sun kammala kada kuri'a ranar Asabar.

" Mun yi watsi da sakamakon zaben da INEC ta sanar, saboda ba shine zabin jama'a ba," a cewarsa.

Shugaban marasa rinjayen ya kara da cewa zaben da INEC ta gudanar ya tabbatar da cewa APC ta rushe ginin dimokradiyya da PDP ya dasa tubalinsa a shekarar 1999.

Sai dai, kakakin majalisar dattijai, Godiya Akwashiki, ya ce akwai dokokin zabe na kasa da suka sanar da mutum abin da zai yi idan bai gamsu da sakamakon zabe ba.

Tuni a sakonsa na taya murna ga 'yan takarar APC da suka samu nasara a zaben, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shawarci wadanda basu gamsu da sakamakon zaben ba da su garzaya kotu domin neman hakkinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel