Yahaya Bello ya sadaukar da nasararsa ga mahaifiyarsa da al'ummar Kogi

Yahaya Bello ya sadaukar da nasararsa ga mahaifiyarsa da al'ummar Kogi

- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sadaukar da nasararsa ga mahaifiyarsa da sauran jama'ar jihar

- Ya kara da yi wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu yayin zaben ta'aziyya

- Ya ce, nasararsa karin kwarin guiwa ce garesa da mataimakinsa kuma ba zasu ba jama'ar jihar kunya ba

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sadaukar da nasararsa a zaben ranar Asabar ga mahaifiyarsa da dukkan jama'ar jihar Kogi.

Gwamnan ya yi magana jim kadan bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana ya kada babban abokin hamayyarsa, Musa Wada na jam'iyyar PDP. Ya mika godiyarsa ga duk wadanda suka taimaka wa jam'iyyarsa ta APC ta yi nasara.

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fadi min a kan Yari - Sanata Yarima

Gwamnan ya yi ta'aziyyar wadanda suka rasa rayukansu tare da alkawarin cewa, makasansu ba zasu tafi ba tare da sun fuskanci fushin hukuma ba.

"A yayin da muke jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu yayin zaben, ina tabbatar muku da cewa sai mun gurfanar da makasansu gaban shari'a don karbar hukuncin da ya dace da su," in ji shi.

Bello ya ce mahaifiyarsa ta taka rawar gani a kaiwarsa wannan matsayin kuma ta cancanci jinjina.

Gwamnan ya tabbatar wa da jama'ar jihar cewa zai koma kan alkawurran kamfen dinsa don cika su. Ya ce, nasarar ta kara musu kwarin guiwa wajen tabbatar da habakar jihar kamar yadda shi da mataimakinsa suka yi alkawari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel