Hukumar Kwastam ta nada sabbin shugabanni, ta yi wa jami'ai 2,408 karin girma (Jerin sunaye)

Hukumar Kwastam ta nada sabbin shugabanni, ta yi wa jami'ai 2,408 karin girma (Jerin sunaye)

- Hukumar kwastam ta kasa ta amince da nada mataimakin shugaban hukumar

- Hukumar ta karawa ma'aikata 2,508 na hukumar matsayi zuwa mataki daban-daban

- Shugaban hukumar ya hori jami'an da su dubi karin girmar a matsayin kalubale

Hukumar kwastam ta kasa ta amince da nada mataimakin shugaban hukuma daya, mataimakansa uku tare da karawa jami'ai 2,508 girma.

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Joseph Attah, ya sanar a ranar Laraba, ya ce karin girman ya fara ne tun daga ranar 1 ga watan Janairu, 2018.

Kamar yadda aka tsara, sabbin wadanda aka kara wa girma sun hada da DCG David Chikan, ACG Kashim Ajiya, ACG Dinatu Umaru da ACG Yusuf Bashar.

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fadi min a kan Yari - Sanata Yarima

Mataimakan da aka kara wa girma sune: AD Sanusi, US Buhari da AI Alfa da sauransu.

Mataimakan shuwagabanni 30 ne aka kara musu girma zuwa shuwagabannin; AC 115 suka koma matakin DC 1; CSC 45 ne aka kara wa girma zuwa AC; DC 43 ne aka kai matsayin CSC.

A yayin taya wadanda suka samu karin girman murna, Col. Hameed Ibrahim Ali ya bukaci jami'an da su dubi karin girman a matsayin wani karin nauyi garesu. Ya bukacesu da kara himma don bunkasa aiyuka tare da sabbin tsare-tsaren hukumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel