Rufe iyakoki: Duk wanda ba zai ci shinkafar 'gida' ba matsalarsa ne - Sanata Adamu

Rufe iyakoki: Duk wanda ba zai ci shinkafar 'gida' ba matsalarsa ne - Sanata Adamu

Shugaban kwamitin Noma na Majalisar Dattawa, Adamu Abdullahi ya ce duk wani dan Najeriya da zai iya cin shinkafar da ake noma wa a kasar ba yayin da ake rufe iyakoki kashashen da ke makwabtaka na kasar shi ya jiyo ma kansa.

Bayan da ya yaba wa shugaban kasa kan jajircewa kan batun rufe iyakokin, ya ce wadanda ke fafutikan ganin an bude iyakokin kasar masu smogul ne da wadanda ke amfana da rusa tatattalin arzikin Najeriya kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Ya ce, "Kasashen dake makwabtaka da mu sun zama hanyoyin da ake amfani da su domin shigo da duk wani irin kaya da suka hada da motocci, kayan abinci kamar shinkafa, masara, dawa, manja, tumatur, kwai da madara.

"Jamhuriyar Benin ta zama daya daga cikin kasashen da suke kan gaba wurin sayan shinkafa a duniya saboda kusancin ta da Najeriya. Kusan dukkan shinkafar da ake sayowa daga Thailand da Indonesia suna shigo Najeriya ne ta Seme Border.

DUBA WANNAN: Kogi: 'Yan sanda sun fadi dalilin da yasa aka kashe shugaban mata na PDP a gidanta

"Saboda haka muna goyon bayan gwamnati a kan wannan tsarin na rufe iyakoki.

"Hakki ya rataya a kan mu na kare kasarmu, duk wanda baya son ya ci shinkafar da ake noma wa a Najeriya, matsalarsa ce."

A ranar 20 ga watan Augusta ne shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin rufe wasu iyakokin kasar na kasa.

Ya ce ya dauki matakin ne saboda yawaitar shigowa da kayayyaki da ake yi cikin kasar ta barauniyar hanya musamman shinkafa.

A cewar shugaban kwastam na kasa, Hameed Ali, hukumarsa na samun harajin kimanin naira biliyan 5.8 a kullum tun bayan rufe iyakokin kasar don hana masu fasakwabri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel