Shegiyar uwar: Wata mata ta jefar da sabon jaririnta cikin Masai

Shegiyar uwar: Wata mata ta jefar da sabon jaririnta cikin Masai

Wata mata mai suna Risikat Olabintan yar jihar Ogun ta jefa sabon jaririn da ta haifa cikin Masai kawai saboda yara sunyi mata yawa.

Tace: "Ina da yara biya da nike wahalan ciyarwa kullum. Mijina ya tafi ya bar ni da su. Saboda haka bana bukatan wani yaron shi yasa ya jefa shi cikin Masai ina haifan shi."

An tattaro cewa Risikat Olabintan, mai zama a unguwar Ibukun Oluwapo a karamar hukumar Owode-Yewa ta jefa jaririn ne da safiyar Lahadi da tayi nakuda.

Cikin ikon Allah, wasu yara dake wasa suka ji kukan yarin daga cikin Masan dake bayan gidan.

Sai al'umman unguwar suka tuntubi yan sanda domin a ceci rayuwar jaririn.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ta bayyana cewa: "A lokacin da aka ceto yaron, babu wanda ya san ita ta aikata abin. Ta haifi yaron a boye misalin karfe 5 na asuba kuma ta jefashi cikin Masai.

"Sai daga baya jami'an tsaro suka gano cewa itace mahaifiyar yaron kuma aka damketa"

Shegiyar uwar: Wata mata ta jefar da sabon jaririnta cikin Masai

Shegiyar uwar: Wata mata ta jefar da sabon jaririnta cikin Masai
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel