Sule Lamido ya bayyana dalilin da yasa Jonathan ya sallama wa APC Bayelsa

Sule Lamido ya bayyana dalilin da yasa Jonathan ya sallama wa APC Bayelsa

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam'iyyar PDP, Sule Lamido ya zargi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da yi wa jam'iyyarsa ta PDP zagon kasa a zaben gwamna da aka kammala baya-bayanan a jihar Bayelsa.

A cikin gajeruwar sakon da mai magana da yawunsa, Mansur Ahmed ya wallafa a Facebook, tsohon gwamnan ya ce Mista Jonathan ya marawa dan takarar jam'iyyar All Progressive Congress, APC baya ne domin kada a bincike rawar da ya taka a badakalar mai na Malabu kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Lamido ya rubuta: "Daga karshe ya sallama jihar Bayelsa da badakalar dallar biliyan 1 ta Malabu don ya tsira da kansa!."

Badakallar ta Malabu ta samu asali ne bayan da kamfanin Shell da ENI sun tura makuden kudi har dallar biliyan 1.1 ta hannun gwamnatin Najeriya a karkashin kulawar tsohon ministan man fetur, Dan Etete.

Kusan rabin kudin ($520 miliyan) ya fada asusun wasu kamfanoni ne dake karkashin ikon Aliyu Abubakar wanda ya mallaki kamfanin AA Oil da ke zargin ya hada baki da gwamnati da Shell da ENI

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fadi min a kan Yari - Sanata Yarima

A cewar wani rahoto da Premium Times ta wallafa, ana zargin tsohon shugaban kasar da hannun wajen yarjejeniyar sayar da rijiyar man OPL 245 da aka kiyasta cewa na samar da ganga biliyan 9 na danye mai ga kamfanonin mai na ENI da Shell a shekarar 2011.

Duk da cewa Shell da ENI sun yi ikirarin cewa ba su san yadda akayi kudin ya fada hannun Mista Etete da abokan huldarsa ba, hujjoji da aka gano sun nuna cewa karya su ke yi.

A halin yanzu ana bincikar Shell, ENI, Mista Etete, Mista Aliyu da wasu ma'aikatan kamfanonin man fetur da dama a kasar Italy kan rawar da suka taka a badakalar.

Wata mai shari'a a Birtaniya ta ce ta gamsu the cewa Mista Jonathan ne wanda ake yi wa lakabi da 'fortunato' a cikin wasu sakonnin kar ta kwana a kan tattaunawar rijiyar man ta OPL 245.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel