Babbar magana: An sace DPO a jihar Adamawa

Babbar magana: An sace DPO a jihar Adamawa

An sace tare da yin garkuwa da Ahijo Myjeli, babban jami'in dan sanda mai kula da ofishin rundunar 'yan sanda da ke karamar hukumar Mubi ta arewa a jihar Adamawa.

A cewar Suleiman Yahaya, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Adamawa, an sace Myjeli ne a kan hanyar Mubi zuwa Maraba da daren ranar Talata.

"An sace shi ne a daura da shingen kan hanyar Mubi zuwa Maraba da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Talata yayin da yake tafiya a cikin motarsa ta kashin kansa.

"Jami'an mu da suka garzaya zuwa wurin sun ji karar harbin bindiga kafin daga bisani su gano motarsa babu kowa a ciki," a cewar kakakin.

Yahaya ya kara da cewa tuni jami'an rundunar 'yan sanda na tawagar yaki da garkuwa da mutane da na tawagar IRT (intelligence response team) suka shiga aiki, inda suka bi sahun masu garkuwa da mutanen domin kubutar da DPO Myjeli.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace mai jego da wasu mutane 5 a cikin garin Kaduna

"Muna fatan cewa zamu samu sakamako mai kyau nan bada dadewa ba, kuma a wannan gaba nake so na yi kira ga jama'a da su taimaka mana da sahihan bayanai a kan 'yan ta'adda duk inda suke, domin daukan mataki a kansu," a cewar Yahaya.

Batun satar DPO Myjeli na zuwa ne a daidai lokacin da aka cika wata guda cif-cif da sace mataimakin kwamishinan 'yan sanda a Kaduna.

An sace Rambo, kwamandan 'yan sanda a ofishin rundunar da ke Suleja, a kan hanyarsa ta zuwa Jos, babban birnin jihar Filato.

Sai dai, ya shaki iskar 'yanci bayan ya shafe sa'a 48 a hannun masu garkuwa da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel