Zaben Kogi: Dino Melaye na yunkurin soke zabe, ya gabatar da bidiyo 21 a gaban INEC

Zaben Kogi: Dino Melaye na yunkurin soke zabe, ya gabatar da bidiyo 21 a gaban INEC

- Sanata Dino Melaye ya bukaci hukumar INEC a cikin wani korafi da ta soke zaben sanata na Kogi ta yamma wanda aka gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba

- Melaye ya gabatar da faifan bidiyo 21 kan magudin zabe da ya wakana a lokacin zabe

- Korafin dan majalisar ya kasance zuwa ga sakatariyar INEC, Rose Orianran-Anthony da kwamishinan zabe na kasa Festus Okoye

Sanata Dino Melaye a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, ya gabatar da wani korafi zuwa ga hukumar zabe mai zaman kanta a Abuja inda ya bukaci a soke zaben sanata na Kogi ta yamma.

Dan Majalisar ya bayyana a shafin Twitter cewa ya gabatar da bidiyo 21 tare da korafinsa a kan batun magudin da ya afku a lokacin zaben.

Sanatan ya ce ya samu tarba daga sakatariyar INEC, Rose Orianran-Anthony da kwamishinan zabe na kasa Festus Okoye.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin 2023: Lanre Razak ya goyi bayan Tinubu ya maye gurbin Buhari

“Kwamishinan INEC na kasa Festis Okoye da sakatariyar INEC yayinda suke karban korafina a yau tare da hujjar bidiyo 21,” ya wallafa a shafin Twitter.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel