Shugabancin 2023: Lanre Razak ya goyi bayan Tinubu ya maye gurbin Buhari

Shugabancin 2023: Lanre Razak ya goyi bayan Tinubu ya maye gurbin Buhari

- Wani jigon jam’iyyar APC, Lanre Razak, ya ce babban jigon jam’iyyar, Bola Tinubu, ne ya fi cancanta ya maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari a 2023

- Razak ya bayyana cewa dashi da sauran masu yiwa Tinubu biyayya sun bukaci jigon na APC da ya yi takarar Shugaban kasar Najeriya a 2023

- Jigon na APC ya ce lallai abunda ke da muhimmanci ga jam’iyya mai mulki shine ganatar da dan takara da ya cancanta ba wai raba tikitin Shugaban kasa na APC zuwa ga wani yanki ba

Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Lanre Razak, ya nuna yakinin cewa babban jigon jam’iyyar na kasa, Bola Tinubu, zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Razak, tsohon kwamishinan sufuri na jihar Lagas kumamamba na kungiyar da ke ba gwamnonin APC shawara, ya fada ma jaridar The Nation a wata hira cewa Tinubu be mutumin da ya dace da wannan aikin.

Ya ce dashi da sauran masu yiwa Tinubu biyayya sun bukaci jigon na APC da ya yi takarar Shugaban kasa a 2023 ko yana so ko baya so.

Tsohon kwamishinan ya bayyana cewa jihar Lagas a yau tana kan cin gajiyar ingancin shugabanci na Tinubu a lokacin da ya yi Gwamnan jihar daga 1999 zuwa 2007.

KU KARANTA KUMA: Kada ka bude iyakokin kasar tukuna – Sanata ya shawarci Buhari

Ya yi watsi da tsarin bayar da tikitin APC zuwa ga kowani yanki, inda ya ce muhimmanci abunda jam’iyyar za ta gabatar shine nagartaccen dan takara da zai iya aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel