Kada ka bude iyakokin kasar tukuna – Sanata ya shawarci Buhari

Kada ka bude iyakokin kasar tukuna – Sanata ya shawarci Buhari

Sanata mai wakiltan Nasarawa ta yamma, Adamu Abdullahi, ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya yi watsi da matsin lambar da ake masa kan bude iyakokin kasar a yanzu.

Abdullahi, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Nasarawa, ya yaba ma Buhari kan tsayawa da ya yi tsayin daka kan matsalolin rashin tsaro.

Ya yi korafin cewa rufe iyakokin kasar na magance matsaloli da dama da suka yiwa kasar katutu, ciki harda tabarbarewar tattalin arziki da cin hanci da rashawa.

Sanatan wanda ya yi jawabi ga manema labarai a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba kan lamarin ya bayyana cewa adawa da rufe iyakokin kasar na zuwa ne musamman daga bangarori biyu.

Ya ce masu fasa kaurin kasashen da ke makwabtaka da kuma masu cin gajiyar rufe iyakokin ne ke matsawa shugaban kasa lamba kan ya sake bude shi.

KU KARANTA KUMA: Kwastam ta kama wani mutum dauke da kudi N2.5m na jabu

Ya bayyana cewa Ya kamata Najeriya ta fara duba rayuwarta kafin duba makomar rufe iyakokin kan makwabta.

Ya ce ya zama dole Najeriya ta gina tubalin cigabanta domin habbaka masana’antunta.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Majalisar dattawa a ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba, ta yi watsi da wata shawara daga Sanata Francis Fadahunsi na neman sanya haramcin shekara biyar na wucin-gadi kan shigo da janareto domin magance rikicin wuta a Najeriya.

Fadahunsi a lokacin wani muhawara kan bukatar da Sanata Chukwuka Utazi, ya gabatar kan bukatar magance matsalar wutar lantarki a Najeriya, inda ya bukaci Majalisar dattawa da ta sanya a cikin ronkonta, haramci kan shigo da janareto na shekara biyar amma takwarorinsa suka nuna adawa da shawararsa.

Sanatoci sun yi watsi da shawarar a lokacin da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya gabatar dashi domin yin zabe akai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel