Babban magana: Dino Melaye ya mika ma INEC bidiyo 21 dake nuna yadda APC ta yi magudi

Babban magana: Dino Melaye ya mika ma INEC bidiyo 21 dake nuna yadda APC ta yi magudi

Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye ya dira babban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, dake babban birnin tarayya Abuja, inda ya nemi INEC ta kashe zaben Sanatan Kogi na yamma daya gudana.

Jaridar Punch ta ruwaito Melaye ya bayyana haka ne yayin da ya shiga ofishin hukumar zaben, inda ya samu tarba daga babba sakatariyar hukumar INEC, Rose Orianran-Anthony da kwamishinan hukumar na kasa, Festus Okoye.

KU KARANTA: Zaman lafiya da kwanciyar hankali sun samu a Najeriya – Sufetan Yansanda

Babban magana: Dino Melaye ya mika ma INEC bidiyo 21 dake nuna yadda APC ta yi magudi

Melaye a INEC
Source: Facebook

Haka zalika Melaye ya mika ma INEC wasu bidiyo guda 21 dake nuna yadda aka yi magudin zabe, tashin hankali da kuma harbe harbe, wanda ya zargi wakilan gwamnatin jahar Kogi da yan APC da aikatawa.

Bayan fitowarsa daga ofishin na INEC, Melaye ya gana da manema labaru, inda ya tabbatar musu da cewa ba zai saurara ba wajen yakin kwato kujerarsa daga hannun APC, don haka “Babu gudu, babu ja da baya.”

A cikin korafin nasa mai take “Kira da a kashe zaben Sanatan Kogi ta yamma daya gudana a ranar 16 ga watan Nuwambar 2019 a wasu yankuna.” Wanda lauyansa Tobechukwu Nweke ya rattafa ma hannu, Melaye yace:

“Daga karshe, duba da yanayin tashe tashen hankulan da aka samu, harbe harbe da kashe kashe, tarwatsa rumfunan zabe, satar akwatunan zabe, dangwale ba bisa ka’ida ba, magudin zabe iri iri, da kuma yi ma tsarin zabe mai inganci zagin kasa kamar yadda muka gani a dukkanin kananan hukumomi guda 7 a cikin wadannan bidiyo..

“Hakan na tabbatar da cewa ba’a yi zaben Sanata a Kogi ba, don haka duba da dokokin zabe na shekarar 2010, muna kira ga INEC ta kashe gaba daya zaben da aka yi da sunan zaben Sanatan Kogi na yamma a ranar 16 ga watan Nuwamba.” Inji shi.

Daga karshe, Festus Okoye ya karbi korafin Dino Melaye a madadin shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu, sa’annan ya bashi tabbacin hukumar za ta yi nazarai a kan haka domin daukan matakin daya kamata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel