DPR ta gano haramtattun matatun man fetur guda biyu a Kano

DPR ta gano haramtattun matatun man fetur guda biyu a Kano

- Hukumar kula da harkoki da hada-hadar man fetur a kasa (DPR) reshen jihar Kano ta gano haramtattun matatun man fetur guda biyu

- DPR ta samu nasarar gano haramtattun matatun ne ta hanyar hada gwuiwa da jami'an tsaron hukumar 'Civil defence'

- Alhaji Musa Zarumi Tambuwal, shugaban ofishin DPR shiyyar Kano da Jigawa, ya ce suna gudanar da bincike a kan haramtattun matatun da aka riga aka rufe bayan gano su

Hukumar DPR mai kula da harkoki da hada-hadar man fetur a kasa, reshen jihar Kano, ta rufe wasu masana'antu guda biyu bisa zarginsu da tace wani sinadari da ake kyautata zaton man fetur ne.

An gano haramtattun matatun man fetur din ne a wasu garuruwa guda biyu da ke yankin karamar hukumar Gezawa a jihar Kano.

DUBA WANNAN: Bayelsa: Gwamna ya fitar da bidiyon yadda magudin zabe ya kasance a Bayelsa

Hukumar DPR ta samu nasarar gano haramtattun matatun ne ta hanyar hada gwuiwa da jami'an hukumar 'Civil defence' (NSCDC) reshen jihar Kano.

Alhaji Musa Zarumi Tambuwal, shugaban ofishin DPR shiyyar Kano da Jigawa, wanda ya jagoranci rufe haramtattun matatun da aka gano, ya ce suna cigaba da gudanar da bincike domin sanin sauran sinadaran da ake tace wa a haramtattun matatun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel