Duniya ina za ki da mu ne? Matashi ya yi garkuwa da budurwa tsawon wata 1 a dakinsa

Duniya ina za ki da mu ne? Matashi ya yi garkuwa da budurwa tsawon wata 1 a dakinsa

Wani matashi dan shekara 18, Yusuf Obaka dake zama a garin Mpape ya sace wata budurwa yar shekara 17 tare da yin garkuwa da ita tsawon wata daya da mako daya, a babban birnin tarayya Abuja.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa matashin ya gurfana gaban wata kotun Ariya ne dake Mpape a Abuja a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, inda ake tuhumarsa da laifin hadin baki tare da satar mutum.

KU KARANTA: Yansandan gona ne suka tayar da hankali a zaben Kogi da Bayelsa – Sufetan Yansanda

Dansanda mai kara, Stanley Nwaforaku ya bayyana ma kotu cewa mahaifin yarinyar, Joseph Ogbeche ne ya kai rahoto ga Yansanda a ranar 17 ga watan Nuwamba a ofishin Yansanda dake Mpape.

Dansandan ya tabbatar ma kotu wanda ake kara ya amsa laifinsa yayin da yake amsa tambayoyi daga wajen Yansanda, inda yace shi da wani abokinsa Shedrack ne suka dauke budurwar tsawon wata daya da mako daya, amma a yanzu zakara ya baiwa abokin sa’a ya tsere.

Dansanda Stanley ya kara ma shaida ma kotu cewa wannan laifin da ake tuhumar Obaka da aikatawa ya saba ma sashi na 97 da 272 na kundin hukunta manyan laifuka na babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai wanda ake kara, Obaka Yusuf ya yi mi’ara koma baya, inda ya musanta aikata laifin. Daga nan Alkalin kotun, mai sharia Salihu Ibrahim ya bada belinsa a kan kudi N200,000, tare da kawo mutum daya da zai tsaya masa a kan N200,000.

Yanke wannan hukunci keda wuya sai Alkalin ya bada umarnin a garkame Obaka a gidan yari har sai ya cika sharuddan beli, sa’annan ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba.

A wani labarin kuma, babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammad Adamu ya bayyana cewa Yansandan da ake zargi sun tayar da hankula yayin zaben gwamnan jahar Bayelsa da na Kogi ba Yansandansu bane, Yansandan gona ne.

Babban sufetan ya bayyana haka ne bayan fitowa daga wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi da manyan hafsoshin hukumomin tsaron Najeriya a ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba a fadar gwamnati.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel