Cika shekaru 62 a rayuwa: Ina jin dadin shawarwarin da kake bani – Buhari ga Jonathan

Cika shekaru 62 a rayuwa: Ina jin dadin shawarwarin da kake bani – Buhari ga Jonathan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan murnar cika shekaru 62 a duniya, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Femi Adesina, wanda yace Buhari tare da sauran yan Najeriya suna yi ma Jonathan addu’ar samun kyakkyawar lafiya da kwazo ta yadda zai cigaba da yi ma Najeriya hidima.

KU KARANTA: Yansandan gona ne suka tayar da hankali a zaben Kogi da Bayelsa – Sufetan Yansanda

Shugaban kasa yana taya iyalai da abokan arzikin Jonathan murnar zagayowar wannan rana, inda ya yaba masa bisa shawarwarin da yake baiwa shuwagabanni a cikin da wajen kasar nan tun bayan daya bar mulki, tare fada musu irin kalubalen daya fuskanta a matakan mulki daban daban.

“Kankan da kai da kishin kasa irin na shugaba Jonathan zai cigaba da amfanar yan Najeriya na tsawon lokaci, tare da tuna musu sadaukarwar da ya yi ma tsarin mulkin dimukradiyya, da kuma samar da cigaba mai daurewa.” Inji shi.

Daga karshe shugaban kasa Buhari ya yi fatan Allah Ya yi ma tsohon shugaban kasa Jonathan tsawon rai.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama wani babban jami’in hukumar kwastam, Bashir Abubakar, mai mukamin mataimakin kwanturolan kwastam sakamakon kin karbar cin hancin makudan kudi da masu fasa kauri suka bashi.

Shi dai Abubakar ya ki amincewa da cin hancin $412,000, kimanin N149,350,000 da wasu mutane suka bashi kimanin watanni 8 da suka gabata domin su shigo da sundukai guda 40 na kwayar nan mai sa maye watau Tramadol.

Da wannan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Abubakar a matsayin jadakan yaki da rashawa, kuma wanda ya zamto abin koyi a tsakanin sauran jami’an hukumar da ma yan Najeriya gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel