Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya jagorancin zaman FEC na farko tun dawowarsa daga Landan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya jagorancin zaman FEC na farko tun dawowarsa daga Landan

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya jagoranci taron majalisar zartarwa FEC karo na farko tun bayan dawowarsa da kasa Ingila.

A fara zaman ne a fadar shugaban kasa misalin karfe 11 na safe.

An kaddamar da zaman ne da addu'a inda ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya gabatar da addu'an mabiya addinin Kirista kuma Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya gabatar da na Musulmai.

Kafin fara tattaunawa a taro, an gudanar da ta'aziyya ga tsohon sakataren gwamnati, Ufot Ekaette, da tsohon ministan labarai, Cif Alex Opeyemi da suka rigamu gidan gaskiya.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sune mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, kusan dukkan ministoci, sakataren gwamnatin tarayya da mai bada shawara kan tsaro, Babagana Munguno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel