Yansandan gona ne suka tayar da hankali a zaben Kogi da Bayelsa – Sufetan Yansanda

Yansandan gona ne suka tayar da hankali a zaben Kogi da Bayelsa – Sufetan Yansanda

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammad Adamu ya bayyana cewa Yansandan da ake zargi sun tayar da hankula yayin zaben gwamnan jahar Bayelsa da na Kogi ba Yansandansu bane, Yansandan gona ne.

Daily Trust ta ruwaito babban sufetan ya bayyana haka ne bayan fitowa daga wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi da manyan hafsoshin hukumomin tsaron Najeriya a ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba a fadar gwamnati.

KU KARANTA: Zaman lafiya da kwanciyar hankali sun samu a Najeriya – Sufetan Yansanda

Sufeta Adamu ya dage kai da fata cewa ba jami’ansu bane, saboda a cewarsa dukkanin jami’an Yansanda suna dauke da wata shaida ta musamman, sa’annan ya kara da cewa zuwa yanzu sun kama mutane 11 dake hannu cikin hare hare, kuma suna cigaba da gudanar da bincike.

Haka zalika Adamu yace koda aka hangi jirgin Yansanda mai tashin angulu yana jefa barkonon tsohuwa a jahar Kogi yayin da ake gudanar da zabe, yace sun yi haka ne kawai domin hana miyagun mutane satar akwatunan zabe da masu fada.

“Mun shirya ma zaben sosai a duk jahohin biyu saboda rahotanni sun tabbatar mana da cewa akwia barazanar tsaro a jahohin, don haka za’a samu tashin hankali. Duk wanda ka gani cikin kayan Sojoji ko kayan Yansanda ba tare da wannan shaidar ba, tabbas na bogi ne, ko kuma ba’a sakashi cikin wadanda zasu yi aikin ba.

“Muna sane da cewa wasu yan siyasa zasu dinka yan barandansu kayan Sojoji da kayan Yansanda, don haka muka kirkiri hanyar da zamu gane Yansandanmu na hakika, domin kuwa sai da muka horas dasu yadda zasu gudanar da aiki a ranar zabe.” Inji shi.

Daga karshe babban sufetan Yansandan ya yi karin haske game da rikicin daya biyo bayan daukan sabbin kuratan Yansanda 10,000, inda yace koda hukumar gudanarwar Yansanda ta kai karar rundunar Yansanda gaban kotu, tuni wadanda aka dauka sun fara samun horo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel