NBS: An samu tashin farashin kaya da 0.36% a cikin Watan Oktoba

NBS: An samu tashin farashin kaya da 0.36% a cikin Watan Oktoba

Alkaluman farashin kaya sun kai 11.61% a cikin watan jiya a Najeriya. Wannan na nufin an samu karin kashi 0.36 a Watan Oktoba. Alkuluman hukumar NBS na kasa ta bayyana mana wannan.

Daily Trust ta rahoto NBS mai tattara alkaluman Najeriya ta na cewa farashin kaya a kasuwa sun tashi daga Watan Satumba zuwa Oktoba. NBS ta wallafa sabon binciken na ta ne a jiyan nan.

Alkaluman wata-wata sun nuna farashin kaya sun karu da kashi 1.07% a Watan jiya. Wannan ya na nufin an samu karuwar tashin farashi da 0.03% daga karin 1.04% da aka samu a Satumba.

Tashin farashin kayan ya fi tasiri a Birane kamar yadda hukumar NBS ta bayyana. Alkaluman farashin kayan masarufi a Birane ya kai 12.20% da kuma kashi 11.07% a cikin Kauyukan kasar.

KU KARANTA: Ana sa ran shigowar jiragen ruwa makil da kayan abinci a Najeriya

A cikin Watan Satumba kuma alkaluman Birane ya tsaya ne a 11.78%, da kuma kashi 10.77%. Sababbin binciken da NBS ta fitar na watan jiya sun nuna cewa kaya na kara tsada ne a ko ina.

Hukumar NBS ta yi karin bayani cewa daga cikin kayan da su ka yi mummunan tashi a cikin ‘yan kwanakin nan akwai nama, burodi, mai, hatsi, dankali, kifi, ganye da doya da dai sauransu.

“An samu karin farashi ne a wajen kayan goge-goge da tufafi, da kayan asibiti da kuma kayan da ake amfani da su a cikin cikin gida.” Inji hukumar ta NBS a Ranar 19 ga Watan Nuwamban 2019.

Wani Masanin tattalin arziki a kasar, Lukman Otunuga, ya shaidawa Daily Trust cewa zai yi wahala babban bankin CBN ya rage riban da ke cikin bashi nan gaba a dalilin tashin farashin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel