Muna roko ku taimaka ku bude iyakokinku - Tsohon shugaban kasar Ghana

Muna roko ku taimaka ku bude iyakokinku - Tsohon shugaban kasar Ghana

Tsohon shugaban kasar Ghana, John Mahama, a ranar Talata ya roki gwamnatin Najeriya ta taimaka ta bude iyakokinta domin yan kasuwan kasashen Afirka ta yamma su cigaba da kasuwancinsu.

Mahama ya bayyana hakan ne yayinda gabatar da jawabi a jihar Legas.

Ya ce rufe wadannan iyakoki ya shafi kananan yan kasuwa musamman a kasashen Kotono, Togo, Ghana, da Kotdibuwa da suka dogara kan kasuwancin kasa da kasa.

Yace: "Ina da tabbacin cewa yan kasuwan da suka dogara kan fitar da kaya wadannan kasashe basu ji da dadi."

"Sakamakon rattaba hannu kan yarjejeniyar kasuwancin bai daya na kasashen Afrika tsakanin Najeriya da makwabtanta, ina son yin amfani da wannan dama wajen rokon Najeriya ta bude iyakokinta saboda kasuwanci ta cigaba."

A makonnin da suka gabata, Ministar harkokin wajen kasar Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey, ta bukaci gwamnatin Najeriya ta taimakawa ta bude iyakarta saboda kayayyakin kasar su rika jiga Najeriya.

Za ku tuna cewa tun watan Agusta, gwamnatin tarayya ta kulle dukkan iyakokinta domin dakile safarar makamai da shinkafa.

Yayinda take ganawa da jakadan Najeriya a Ghana, Olufemi Abikoye, ministar ta ce har yanzu kayayyakin Najeriya na shiga Ghana.

Ta ce gwamnatin Ghana za tayi amfani da dukkan wani faka ta diflomasiyya domin tabbatar da cewa Najeriya ta bude iyakokinta ga kasashen dake makwabtaka da ita domin shigowan kayayyaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel