Kwastam ta kama wani mutum dauke da kudi N2.5m na jabu

Kwastam ta kama wani mutum dauke da kudi N2.5m na jabu

- Hukumar kwastam ta sanar da kama wani mutum dauke da kudaden jabu da ya kai kimanin naira miliyan 2.5.

- Kwamandan rundunar reshen, Michael Agbara, ya ce an kama mai laifin ne a lokacin gudanar da aikin killace iyakokin kasar da kuma bayanai da suka samu daga mutanen da ke garuruwan iyakokin

- Su kan ida mugun nufinsu ne a kan mutane ma su chanja sabbin kudi

Jami’an hukumar kwastam na Najeriya a reshen Ogun a ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba, sun kama wani mutum dauke da kudaden jabu da ya kai kimanin naira miliyan 2.5.

Kwamandan rundunar reshen, Michael Agbara, ya ce an kama mai laifin ne a lokacin gudanar da aikin killace iyakokin kasar da kuma bayanai da suka samu daga mutanen da ke garuruwan iyakokin.

Agbara ya kara da cewa mai laifin na fakon bayin Allah wadanda kan chanja kudade zuwa sabbi.

“Ya ce su biyu ne amma dayan mutumin ya tsere. Dukkanin kudaden nan na jabu ne, su kan yaudari mutane da ke son canja kudade zuwa sabbi. Idan har ka shiga hannunsu toh sai sun damfare ka.

“Wannan babban ta’addaci ne,” in ji Agbara.

Rundunar ta kuma kama diro 40 na barasa da aka yi fasa kaurinsu zuwa kasar ta iyakar Idiroko daga kasar Benin.

KU KARANTA KUMA: An yi asarar naira tiriliyan daya kan ayyukan mazabu a shekara 10 - Buhari

Ya yi Allah wadai da aikin ta’addanci na shigo da ethanol wanda a cewarsa mazanbata na hada shi da ruwa sannan su saida wa mutane a matsayin barasa.

Agbara wanda ya kuma bayyana cewa kotu za ta haramta ethanol yayinda za a hukunta mai laifin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel