Bayelsa: Gwamna ya fitar da bidiyon yadda magudin zabe ya kasance a Bayelsa

Bayelsa: Gwamna ya fitar da bidiyon yadda magudin zabe ya kasance a Bayelsa

A ranar Talata ne Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson ya yi watsi da sakamakon zaben gwamnoni da aka yi a ranar Asabar.

Ya fitar da bidiyon magudin da ake zargin anyi a akwatunan zabe don tabbatar da ikirarinsa na magudi da tashin hankula da aka yi.

A yayin magana da taron manema labarai, ya kwatanta zaben da dabarar kwace Bayelsa ta karfin tsiya tare da dora jam'iyya mai mulki a karagar jihar.

Ya kushe hada kai da aka yi tsakanin jami'an tsaro da 'yan daba wajen kwace kayayyakin zabe a kananan hukumomin jihar.

Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin APC ta tarayya da ta dau mummunan mataki wajen tsare damokaradiyya tare da hakkin kowanne dan Najeriya wajen zabe.

DUBA WANNAN: Yadda bindigar shaida ta harbe lauya a kotu

Ya ce: "Ba wannan bane karo na farko da muka fara zabe a jihar nan. An kashe mutane, wasu kuma an wurgasu ruwa amma har yanzu babu abinda aka yi musu.

"A matsayinmu na wadanda suka yarda da damokaradiyya, yakamata muyi amfani da salon damokaradiyya don kalubalantar abinda ya faru a Ogbia, Ijaw ta Kudu da Nembe. Don duk sakamakonsu na bogi ne. Abinda aka yi kawai fyade ne ga damokaradiyya Bayelsa,

"Juyin mulki ne aka yi a Bayelsa. Karshen hadin kai wajen cuta shine yadda gwamnatin tarayya ta hada kai da cibiyoyin tsaro wajen take hakkin mutanen jihar,

"Ba a taba yin abu makamancin haka ba. A 2015, abun bai kai haka ba. A wannan kuwa, ba sojoji kadai aka umarta wajen kwace Bayelsa ba, har da 'yan dabar APC wadanda suka saka tsoro a zukatan jama'a,"

Hakazalika, Dickson ya ce zai shirya kwamitin mika mulki ta yadda zai mika mulki cikin lumana a ranar 14 ga watan Fabrairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel