Jiragen ruwa cike da man fetur da abinci za su iso Najeriya - NPA

Jiragen ruwa cike da man fetur da abinci za su iso Najeriya - NPA

Hukumar NPA mai kula da tashoshin ruwan Najeriya ta ce ta na sa ran shigowar wasu jirage masu dauke da kayan abinci da tacaccen man fetur da wasu kayan a tashoshin ta da ke Legas.

Kamar yadda NPA ta bayyana, jiragen ruwa 25 ne za su fara sauka a tashoshin Apapa da na Tin Can Island da ke Garin Legas daga tsakiyar wannan watan na Nuwamba zuwa karshen bana.

Ana tsammanin kayan za su shigo Najeriya ne daga Ranar 16 ga Watan Nuwamba zuwa Ranar 31 ga Disamba mai zuwa inji hukumar NPA ta kasar a wasu takardu da su ka fitar kwanan nan.

Jirage tara za su shigo da kayan karafuna da motoci da sukari ne da wasu kayan masarufi. Wasu jiragen ruwa 17 kuma za su shigo da kayan man fetur da aka tace a matatun kasashen ketare.

KU KARANTA: Buhari ya yi muhimmin zama da Hafsun Sojojin Najeriya

Wadannan jirage su na dauke ne da fetur, kananziri, da gwagwanin dauko kaya. Akwai kuma jiragen da ke tashoshin kasar su na jira su sauke masu alkama da sukari da wasu kayan abinci.

Rahotannin na yau Ranar Laraba 20 ga Watan Nuwamban 2019 sun ce wadannan jirage su na tafe da kwangiri da sauran karafuna da ake amfani da su a manyan masana’antu da kamfanoni.

Yayin da wasu jiragen su ka kamo hanya, wasu kuma su na zaune a tashar su na jiran ranar da za a sauke kayan da su kawo. Gwamnatin Najeriya ta sa takunkumi wajen shigo da wasu kayan.

Idan ba ku manta ba kuma gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta rufe kan iyakokin kasa domin maganin fasa-kauri. Wannan mataki da aka dauka, ya gallazawa makwabtanta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel