An yi asarar naira tiriliyan daya kan ayyukan mazabu a shekara 10 - Buhari

An yi asarar naira tiriliyan daya kan ayyukan mazabu a shekara 10 - Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya zargi yan majalisa da kashe naira tiriliyan 1 kan ayyukan mazabu cikin shekara 10 ba tare da ganin wani sakamako mai kyau ba

- Buhari ya bayyana cewa bayanan da ya karba kan ayyukan mazabu a yankunan karkara sun nuna cewa ayyukan ba wani tasiri da suka yi ga al'umma

- Ya umurci ICPC da ta bibiyi yan kwangila da suka karbi kudade domin wadannan ayyuka da kuma masu mara masu baya a gwamnati

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sama da naira tiriliyan 1 da mambobin majalisar dokokin tarayya suka kashe kan ayyukan mazabu a shekaru 10 da suka gabata ba su haifar da kowani sakamako ba.

Buhari ya fadi hakan ne a lokacin da yak e jawabi a wani taron yaki da cin hanci da rashawa a ma'aikatun gwamnati wanda aka fara a jiya Talata, 19 ga watan Nuwamba a fadar Shugaban kasa.

Ya kuma bayyana cewa bayanan da ya karba kan ayyukan mazabu a yankunan karkara sun nuna cewa ayyukan ba wani tasiri da suka yi ga al'umma.

Ofishin sakataren gwamnatin tarayya, oss Mustapha, tare da hadin gwiwar hukuma yaki da rashawa ta ICPC ne suka shirya taron.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta yi wasti da bukatar sanya haramci kan shigo da janareto

Ya umurci ICPC da ta bibiyi yan kwangila da suka karbi kudade domin wadannan ayyuka da kuma masu mara masu baya a gwamnati.

A baya mun ji cewa a ranar Talata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika wasu kudiri 6, masu nasaba da harkar jiragen sama, zuwa majalisar dattijai domin mayar da su doka.

Sabbin kudiran 6 sune; ' Civil Aviation Bill, 2019; Federal Airports Authority of Nigeria Bill, 2019 and Nigerian College of Airspace Management Agency (Establishment) Bill, 2019.

Sauran sun hada da 'Nigerian College of Aviation Technology (Establishment) Bill, 2019; Nigerian Meteorological Agency (Establishment) Bill, 2019 and Nigerian Safety Investigation Bureau (Establishment) Bill, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel