APC na amfani da Jonathan wajen halasta damfara, in ji Dickson

APC na amfani da Jonathan wajen halasta damfara, in ji Dickson

Gwamnan jihar Bayelsa, Mista Seriake Dickson, ya bayyana cewa shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na amfani da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan wajen halasta zambar zabe da ya zargi jam’iyya da aikatawa a zaben gwamna da aka kammala kwanan nan a jihar.

Dickson, wanda ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labarai a Yenagoa a ranar T6alata, 19 ga watan Nuwamba, ya ce yunkurin wani dabara ne da shugabannin APC suka shirya domin tabbatar da rashin daidai da kuma kwace jihar Bayelsa ta karfi da yaji.

Wasu shugabannin APC, ciki harda zababben gwamna, David Lyon; gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru; Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu da kuma karamin ministan man fetur, Timipreye Sylva, sun ziyarci Jonathan bayan APC ta lallasa PDP a zaben gwamnan Bayelsa.

Amma Dickson ya ce shugabannin APC na sane da cewar Jonathan bai taimaka ba wajen magudin da suka yi a tsarin zabe domin samun nasara a kan PDP.

Dickson wanda ya bayyana cewa yana da karfin gwiwa a kan cewa bangaren shari’a za ta yi adalci kan lamuran da aka samu kafin zaben, ya yi kira ga mutane da su nuna dattako sannan kada su yarda su fada cikin rikici.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta yi wasti da bukatar sanya haramci kan shigo da janareto

A baya Legit.ng ta rahoto cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben da aka kammala kwanan nan a jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta kaddamar dashi a matsayin wanda ya lashe zabe.

INEC a ranar Lahadi ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar APC, Cif David Lyon, a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan ya samu kuri’u 352,552 wajen kayar da babban abokin adawarsa, Douye Diri na PDP wanda ya samu kuri’u 143,172.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel