Majalisar dattawa ta yi wasti da bukatar sanya haramci kan shigo da janareto

Majalisar dattawa ta yi wasti da bukatar sanya haramci kan shigo da janareto

- Majalisar dattawa a ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba, ta yi watsi da wata shawara da ke neman sanya haramcin shekara biyar na wucin-gadi kan shigo da janareto

- Sanata Francis Fadahunsi ne ya gabatar da wannan shawara domin magance rikicin wutar lantarki a Najeriya

- Sai dai majalisar dattawan, ta bukaci kwanitinta kan wutar lantarki da ya binciki ayyukan kamfanonin rarraba wutar lantarki tare da kudirin gano abunda ke haddasa rashin samun wuta a Najeriya

Majalisar dattawa a ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba, ta yi watsi da wata shawara daga Sanata Francis Fadahunsi na neman sanya haramcin shekara biyar na wucin-gadi kan shigo da janareto domin magance rikicin wuta a Najeriya.

Fadahunsi a lokacin wani muhawara kan bukatar da Sanata Chukwuka Utazi, ya gabatar kan bukatar magance matsalar wutar lantarki a Najeriya, inda ya bukaci Majalisar dattawa da ta sanya a cikin ronkonta, haramci kan shigo da janareto na shekara biyar amma takwarorinsa suka nuna adawa da shawararsa.

Sanatoci sun yi watsi da shawarar a lokacin da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya gabatar dashi domin yin zabe akai.

KU KARANTA KUMA: Abinda Buhari ya fadi min a kan Yari - Sanata Yarima

Sai dai majalisar dattawan, ta bukaci kwanitinta kan wutar lantarki da ya binciki ayyukan kamfanonin rarraba wutar lantarki tare da kudirin gano abunda ke haddasa rashin samun wuta a Najeriya.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa a ranar Talata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika wasu kudiri 6, masu nasaba da harkar jiragen sama, zuwa majalisar dattijai domin mayar da su doka.

Sabbin kudiran 6 sune; ' Civil Aviation Bill, 2019; Federal Airports Authority of Nigeria Bill, 2019 and Nigerian College of Airspace Management Agency (Establishment) Bill, 2019.

Sauran sun hada da 'Nigerian College of Aviation Technology (Establishment) Bill, 2019; Nigerian Meteorological Agency (Establishment) Bill, 2019 and Nigerian Safety Investigation Bureau (Establishment) Bill, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel